Shayeshaye wata abace wadda tazama ruwan dare a tsakanin matasa musamman yan kasa da shekara talatin 30, shaye shayen ya kunshi tabar wiwi,giya , miyagun kwayoyi da sauransu.
Ayau matasa sun dauki shayeshaye wata hanyace ta burgewa wacce idan bakayi awasu guraren ana daukarka kamar baka waye bane, abin bakin ciki ma shine harda mata kai abin mamakinma wai matan aure, kiyasi yanuna a kullun ana samun masu fadawa cikin harkar ,, kiyasi ya nuna cewa akwai kashi hamsin da shida maza wadanda suke taammali da miyagun kwayoyi sannan kashi arbain da hudu mata,
Yanda ake ta'ammali da miyagun kwayoyi a Kano ya kai matsayin da mutum zai iya zuwa duk wajen da ake sai da kwaya ko ganye ya saya a fili ba tare da yana jin kunyar jama'a suna ganinsa a matsayin mai shan miyagun kwayoyi ba.
Unguwanni irin su Ireland a kofar Nasarawa da Koki da kofar Dan Agundi da kofar na Isa da Tudun Murtala da kasuwar Takari a Burget da Fage layin Kamfala da Kofar Ruwa na daga dimbin wuraren da ake sayar da irin wadannan kayan maye a fili ba kunya ba tsoro.
Lamarin ya kai har an taba yin wata cacar shan kwayoyi masu dinbin yawa a cikin shayi a Kofar ruwa, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar daya daga masu cacar.
Wani matashi da ke mu'amilla da kwayoyin ya shaidawa wakilin mu cewa, suna samun kwayoyin ne a kasuwar Sabon Gari.
kuma jin haka yasa wakilinmu garzayawa kasuwar ta Sabon Gari don jin ta bakin kwamitin rikon shugabancin kungiyar masu saida magani, ko suna sane da cewa ana saida haramtattun kaya a wajensu?
Inda Malam Yusuf Bala Kibiya mamba a kwamitin, ya musanta cewa suna saida miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa suna hukunta duk wanda aka samu yana saida kwayoyin da aka haramta kamar yadda tsarin kasuwar ya tanada.
"Dimbin jama'a ne ke sha da sayar da irin wadannan kayan maye a fili ba kunya ba tsoro"....
inji wakilinmu na duniyarmu a yau
ILLOLIN SHAYESHAYE
1- kashe garkuwan jiki2-rikicewar bugawan zuciya
3- hauka
4- ciwon kuhu
5- saurin fushi



Comments
Post a Comment